Pages

Saturday 22 June 2019

Amfanin ganyan mangwaro 10 a jiki da yadda za a iya sarrafa shi don magani

Mangwaro na daga cikin ‘ya’yan itatuwan da ake ciki wanda ke dauke da sinadarorin inganta kiwon lafiyar mutum.


A cikin mangwaro akwai ‘Vitamin C wanda ke warkar da mura, rauni da sauran su sannan akwai copper wanda ke kare mutum daga kamuwa da cututtuka, potassium wanda ke inganta motsa jiki da magnesium wanda ke kaifafa kwakwalwa.

Bayan haka likitoci sun bayyana cewa ganyen mangwaro ma na dauke da sinadarorin dake inganta kiwon lafiyar mutum.

Bayanai sun nuna cewa nahiyar Asia sun fi yin amfani da ganyan mangwaro wajen warkar da cututtuka saboda ingancin da yake da shi.

Ga amfani 10 da ganyan yake da shi

1. Ganyen mangwaro na kawar da cutar siga wato ‘Dibetes’

Ganyan mangwaro na warkar da cutar siga ne idan aka shanya shi ya bushe sannan aka jika garin a ruwa sai a rika sha.

2. Yana kawar da hawan jini.

Ana yin amfani da garin busashen ganyen mangwaro, sai a rika diba ana dafa shi an sha kamar shayi. Haka zai taimaka wajen kawar da hawan jini.

3. Yana warkar da cutar koda

Shan ruwan ganyen magwaro da aka jika na warkar da cutar Koda.

4. Yana warkar da matsalolin da ke han numfashi.

Idan aka hada ruwan ganyen mangwaro da zuma, ana samun lafiya ga mura da cutar Asma.

5. Yana kawar da atini.

Shima idan aka sha ruwan zai taimaka wajen dakatar da Atini.

6. Yana dakatar da shakuwa.

Mai fama da shakuwa zai warke idan ya shaki hayakin ganyen mangwaro.

7. Mai fama da rashin natsuwa wato ‘Anxiety’ zai samu sauki idan yana shan ruwan ganyan mangwaro.

8. Mai fama da ciwon ciki zai sami sauki idan yana shan ruwan dafaffen ganyen kullum safe kafin a ci abinci.

9. Yana warkar da ciwon kunne.

Ruwan dake cikin ganyen mangoro na dauke da sinadarin warkar da ciwon kunne wanda idan aka diga a kunnen dake ciwo zai warke.

10. Ganyen mangwaro na warkar da kuna

Ana amfani da tokan ganyen mangwaro a shafa a kan rauni don a warke.
Premiumtimeshausa.



No comments:

Post a Comment