Pages

Tuesday 25 June 2019

Gwamnatin Jihar Gombe Ta Bayyana Sarkin Gombe A Matsayin Amirul Hajjin Bana

Mai girma gwamnan jihar Gombe Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya ya amince da nadin Sarkin Gombe Dr Abubakar Shehu Abubakar lll, a matsayin Amirul Hajjin wannan shekara ta 2019.


A wata takardar manema labaru da ta fito ta ofishin gwamnan dauke da sa hannun mai taimakawa gwamnan ta bangaren yada labaru Isma'il  Uba Misilli, gwamnatin jihar ta tabbatar da Basaraken a matsayin wanda zai jagoranci tawagar jihar Gombe zuwa aikin Hajjin bana.

Takardar na kunshe da sunayen karin wasu mutane a matsayin wanda zasu takewa Basaraken baya yayin gudanar da aikin, tawagar ta hada da Chiroman Gombe, Bala Waja, Malamai da sauran su.
Daga Haji Shehu.


No comments:

Post a Comment