Pages

Saturday 22 June 2019

Nima zan kalli wasanku, ku maida hankali>>Shugaba Buhari ya karfafawa Super Eagles gwiwa

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bukaci 'yan kwallon Najeriya na Super Eagles da suke a kasar Egypt wajan gasar cin kofin Nahiyar Afrika da su mayar da hankali dan cin wasanninsu a gasar.



A sanarwar da me magana da yawun shugaban kasar, Femi Adesina ya fitar ya bayyana cewa, Shugaba Buhari yace, shima zai kalli wasan kamar kamar yanda sauran miliyoyin 'yan Najeriya zasu kalla.

Ya kara da cewa, zamu baku duk goyon bayan da ya kamata kuma zamu karfafa muku gwiwa.

Ya bayyana cewa ciwo kafin ne kawai zai farantawa 'yan Najeriya rai, yace kwallo na daya daga cikin abinda ke hada kan 'yan Najeriya kuma yana bukatar Super Eagles da su mayar da hankali wajan ganin sun sawa Najeriya farin ciki dan samun saukin matsalolin da suke fuskantarsu wanda gwamnati na iya bakin kokarinta waja magainsu.

Shugaban ya kuma jawo hankalin 'yan kwallon da su bi dokar kwallo a wasannin da zasu buga.

No comments:

Post a Comment