Pages

Tuesday 25 June 2019

Wasu rahotannin satar Mutane a Najeriya ba gaskiya bane>>Osinbajo ya gayawa 'yan Najeriya a Amurka

Mataimakin shugaban kasa,Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana cewa wasu daga rahotannin sace mutane dan neman kudin fansa a Najeriya ba na gaskiya bane, ya bayyana hakane wa 'yan Najeriya mazauna kasar Amurka.



Osinbajo da ya je kasar Amurka inda yake son ganawa da mataimakin shugaban kasar Mike Pence yayi wata ganawa ta musamman da 'yan Najeriya mazauna kasar ta Amurka inda ya shaida musu cewa maganar satar mutane dan neman kudin fansa ba sabon abu bane.

Kai wasu ma labaran satar mutanen da ake yayatawa bana gaskiya bane, ana zuzutasu ne saboda siyasa, sannan kafafen sadarwa na zamani suma suna taimakawa wajan karawa miya gishiri a kan maganar satar mutane.


Ya kara da cewa duk labarin satar mutane dan neman kudin fansa da suka samu sukan yi kokarin bincikawa dan tabbatar da gaskiyarshi amma wani lokacin zaka samu karyane.

No comments:

Post a Comment