Pages

Monday 24 June 2019

Yanda Gwamna Yahaya Bello ya dauki dan fashi kuma gawurtaccen me kisan mutane dan taimakawa shugaba Buhari cin zabe a jihar Kogi

Wani rahoto ya bayyana yanda gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello ya dauki wani tsohon dan fashi kuma gawurtaccen me kashe mutane dan taimakawa shugaban kasa, Muhammadu Buhari cin zabe a jihar ta Kogi.



Rahoton na Sahara Reporters ya bayyana Abdulkareem Abubakar wanda ake kira da Ijogbon watau matsala, tsohon dan fashine kuma me wa 'yan siyasa aiki wajan kashe mutanen da suka zamar musu matsala.

Rahoton yace, Ijogbo yayi aiki da manya-manyan 'yan siyasar jihar ta Kogi da suka hada da tsaffin gwamnoni da ciyamomi. Rahoton yace Ijogbon na aiki da 'yansanda wajan bashi bayanan sirri, wanda hakane ke sa ba'a iya kamashi.


Akwai lokacin da kwamishinan 'yan sandan Kogi ya kirashi ya bashi shawarar ya zo a musu afuwa su ajiye makamansu in kuma ba haka ba za'a nemeshi ruwa a jallo, kuma ya yadda ya ajiye makanmai shi da yaranshi.

Saidai hakan ya zamar mai matsala saboda 'yan siyasa da dama sun san cewa yasan sirrin ta'asar da suka sa shi ya tafka a baya, dan haka suka tura a kasheshi amma ba'a yi nasara ba.

Wanda aka tura ya kasheshi din ya kashe mai 'yar uwa da dan uwa dan haka shima sai ya kasheshi, dalilin kashe wanda aka aika ya kasheshine sai 'yansanda suka kamashi akace za'a mai shari'a.


Ba'a sake jin duriyarshi ba, kwatsam kuma sai gashi da gwamna Yahaya Bello da shugaba Buhari,lokacin yakin neman zabe.

Wannan yasa da labarin ya bayyana sai Sahara Reporters ta yi kokarin jin ta bakin 'yansanda yanda shari'ar Ijogbon ta kaya amma suka ki cewa uffan.

Sahara Reporters ta ruwaito cewa Ijogbon yanzu yana cikin kwamitin yakin neman zaben Yahaya Bello.

No comments:

Post a Comment