Pages

Sunday 14 July 2019

Kotu ta kara bada belin Sambo Dasuki, ta hana sake tsare shi

Kotun Daukaka Kara ta sake bayar da belin tsohon Mashawarcin Shugaban Kasa a Fannin Tsaro, Sambo Dasuki.


Sannan kuma kotun ta umarci gwamnatin tarayya ta biya Dasuki naira milyan 5 a matsayin diyyar tsare shi da aka yi, wanda ya kauce wa Tsarin Dokar Kasa Sashe na 35 (6), wanda ya bai wa kowane dan Najeriya ‘yancin walwala.

Tun cikin watan Disamba, 2015 ake tsare da Dasuki, a kan zargin salwantar dala bilyan 2.1, kudin da aka ce an ware domin sayen makaman yaki da Boko Haram.

Kotu ta sha bayar da umarni ba sau daya ko sau biyu ba, cewa a sake shi a karkashin beli, amma gwamnatin tarayya ta yi biris da umarcin kotun.

PREMIUM TIMES ta samu kwafen hukuncin da kotu ta yanke a jiya Juma’a, 13 Ga Yuli, inda ta jingine wancan sharuddan beli na baya da kotuna suka bayar na ajiye kudi naira milyan 100 daga masu beli mutum biyu, aka maida shi zuwa na mai kadarar naira milyan 100 kawai a Abuja.

Lauya Ahmed Raji na ofishin lauyoyin da ke kare Dasuki, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa sun kai kara ne kotu, inda suka yi korafin cewa sharuddan belin da aka kakaba wa Dasuki ya yi tsauri sosai.

Lauya Adeola Adedipe, wanda ya shigar da korafin a kotu, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa a baya an sha bayar da belin Dasuki, amma a bisa sharudda masu tsauri.

“Ko an cika sharuddan ma ba su sakin sa.” Inji shi.

Ya ce an bayar da sharuddan belin naira milyan 100 a baya amma ba a sake shi ba.

Ya ce wannan sharadin beli na yanzu kuwa, na alkawarin ajiyar takardun shaidar kadarar akalla da ke da darajar kudi nair milyan 100 a Abuja (bond). Wato ba ba na kai ajiyar kudi ba ne zunzurutun su a kotu.

Daga cikin sharuddan belin can baya baya ga ajiyar zunzurutun kudi naira milyan 100 a kotu, an nemi Dasuki ya samo ma’aikatan gwamnatin tarayya biyu masu mukamin da bai kasa ga matakin albashin ‘Level 16’ ba. Kuma kowane mai beli ya kasance mazaunin Abuja ne, ba shigowa ya ke yi ya koma ba.

Sannan kuma idan dan kasuwa ne, to ya kasance sai mai gida a Abuja. Kuma idan an kai kudin belin, za a ci gaba da ajiyar su a hannun rajistara na kotu, har sai ranar da aka kammala shari’a sannan a bai wa mai belin kudin sa.

Wannan ne ya sa lauyoyin Dusuki ba su gamsu da sharuddan ba, suka garzaya Kotun Daukaka Kara a cikin watan Yuli.

KOTU TA HARAMTA SAKE TSARE DASUKI

A yanzu kotu ta haramta sake kama Dasuki a tsare shi. sannan kuma ta ce a duk lokacin da ake neman sa a yi masa wasu tambayoyi, to a kira shi da rana, a lokacin aiki, tsakanin karfe 9 na safe zuwa 6 na yamma. Kada a sake a kira shi da dare. Idan ya je kuma kada a sake ya haura karfe 6 na yamma bai fice daga ofishin jami’an tsaro ba.

Kotu ta ce a rike fasfo na Dasuki idan an sallame shi, kuma rajistara ya shaida wa gwamnatin tarayya da zarar Dasuki ya cika sharuddan beli, domin a gaggauta sakin sa.


No comments:

Post a Comment