Pages

Wednesday 17 July 2019

Na Goyi Bayan Fulani Su Dawo Gida Arewa Idan Za A Ci Gaba Da Cin Zarafin Su A Yankunan Kudu>>Farfesa Ango Abdullahi

Shugaban kungiyar Dattawan Arewa, Farfesa Ango Abdullahi ya goyi bayan Fulani makiyaya da su tattaro shanunsu da duk wasu kadadrori da suka mallaka a yankunan Kudu su dawo yankin Arewa idan har za a ci gaba da cin zarafin su a yankunan kudu.


Farfesa Ango Abdullahi wanda ya bayyana hakan a yayin hirarsa da RARIYA, inda ya kara da cewa a ra'ayin sa yin hakan shi zai zama mafita ga irin barazanar da wasu shugabannin kudu da tsagerun su suke yi wa Fulani makiyaya dake zama a can.

Farfesa ya ce bai ga dalilin da ya sa Fulani za su je yankin kudu yin kiwo ba saboda arewa ita ke da kashi 70 zuwa 80 na fadin kasa. 

"Mu muka jawo Fulani suka je yankunan da ba a san su ba har ta kai ga ana wulakanta su. Domin mu muka kashe burtulolin su da sauran wurin da za su yi kiwo".

"Ko Bature da ya zo Nijeriya ya gano cewa noma da kiwo ne za su rike kasar ba wai wannan gurbataccen man fetur din da muke tinkaho da shi ba a yanzu.

Farfesan ya kuma bayyana dalilin da ya sa ya goyi bayan gamayyar kungiyar matasan Arewa a lokacin da suka baiwa kabilar Inyamurai wa'adin wata uku da su bar yankin arewa, inda ya ce ba komai ya sa ya goyi bayan matasan ba sai do yadda tsagerun yankin kudu da shugabannin su suke cin mutuncin iyaye da kakannin al'unmar yankin arewa.

Ya ce goyon bayan da suka nuna game da matakin da matasan suka dauka a lokacin,shi ya sa aka nemi sulhu. 

"Lokacin da yaranmu suka soma nuna rashin jin dadin su game da kalaman da tsagerun kabilar Ibo suke furtawa a kan Arewa, ai an samu wasu daga cikin shugabannin arewa da suka soma barazanar kama su. Sai muka nuna cewa saidai a kama har da mu iyayensu",  cewar Ango Abdulahi.

Ango Abdullahi ya kara da cewa an samu 'yan arewa da son zaman lafiya amma duk da haka sune aka maida abin tsana kuma ake cuta.

"Duk da dokar kasa ta bada damar a bunkasa kowace yanki, amma an bar arewa a koma baya. Kuma hakan ba laifin kowa bane, laifin mu ne mu mutanen arewa. Saboda mun ki junanmu. Don haka bana tunanin wani zai so mu.

Farfesa Ango ya kara da cewa sun gana da shugaban gwamnonin Arewa, wato Gwamna Simon Larlung na jihar Filato game da matsalar ta Fulani da makiyaya, inda gwamnoni da dama suka bayyana cewa sun shirya samarwa da makiyaya wurin da za su gudanar da kiwo.

Farfesan ya kara da cewa suna sane da yadda aka soma kai hari ga rugagen Fulani a wani sashe na jihar Ogun. Don haka ya yi kira ga shugabanni Fulani da su kasance masu bibiyar duk wani mawuyacin yanayi da makiyaya suke ciki a kasar nan, wanda idan akwai bukatar su dawo gida Arewa sai su dawo kafin a cimma matsaya. 

Farfesan ya kuma goyi bayan gwamnati da ta kafa wani kwamiti na musamman domin biyan diyya ga dukkan bangarorin da rikicin fulani da manoma ya shafa, sabanin yadda wasu tsiraru suke fitowa kafafen jaridu suna neman gwamnati ta biya diyya ga manoma kadai. Inda ya kara da cewa ba manoma kadai bane suka yi asarar dukiyoyi da rayuka ba, su ma fulani sun yi asara.

Farfesan ya ce idan ma gwamnati ta amince za ta biya diyyan, akwai bukatar a kafa kwamiti mai dauke da adalan mutane wadanda za su yi wa dukkan bangarorin adalci ba tare da nuna bambanci ba.
Rariya.


No comments:

Post a Comment