Pages

Thursday 18 July 2019

Sheik Zakzaky Zai Iya Rasa Dayan Idonsa Daya Da Ya Rage Idan Ba A Dauki Matakin Gaggawa Ba>> Barista Falana

Lauya mai zaman kan sa Barista Femi Falana SAN, ya ce muddin ba a dauki matakin da ya dace cikin gaggawa ba, jagoran 'yan Shi'a Sheikh Ibrahim Zakzaky zai iya rasa dayan Idanun sa da ya rage.


Lauyan Gwamnati Barista Dariye, ya ce kotu ta zauna a yau ne domin duba takardun da masu kariya suka shigar na neman a bar Sheikh Zakzaky ya fita kasar waje domin neman magani kamar yadda suka bukata.

Dariye ya kara da cewa "bayan mun tafka muhawara kan yiwuwar barin Shehin Malamin tafiya kasar waje a gaban kotu, sai Alkali ya bada damar kowana bangare ya binkici takardun da Likitoci suka mikawa kotu bayan sun kammala binkicensu.

Inda daga karshe kotu ta dage sauraron wannan bukata zuwa ranar 29 ga watan Yulin da muke ciki na shekarar 2019, domin yin hukunci a kan tafiyar Malam kazar Indiya, wajen duba lafiyar sa kamar yadda masu kariya suka bukata ko akasin haka".

In baku manta ba dai, a baya mun kawo muku yadda Gwamnatin Jihar Kaduna ke tuhumar Sheikh Zakzaky da matar sa Zeenatu da wasu mutum biyu da hannu a aikata laifin kisan kai, da yin taro ba bisa ka'ida ba, wanda kotun ta dage sauraron karar har Illa ma sha Allah.

Bayan zaman kotu na yau 18 ga watan Yulin nan da muke ciki, Barista Falana SAN ya ce Sheikh Zakzaky na cikin wani hali na tsananin rashin lafiya, wanda hakan na iya haddasa masa rasa dayan idon da ya rage muddin ba a dauki matakin da ya dace akan lokaci ba.
Rariya.


No comments:

Post a Comment