Pages

Tuesday 16 July 2019

SHUGABA BUHARI YA RATTABA HANNU A KAN A FARA BIYAN SABON TSARIN ALBASHI A YAU TALATA

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rattaba hannu don biyan sabon kudin albashi ga ma’aikatan da suke daukar albashin kasa da 30,000.


Shugaban hukumar kula da albashi, Chief Richard Egbule ne ya bayyana haka a lokacin da ake gudanar da taro akan kaddamar da fara biyan albashi sabon albashin na N30,000.

Chief Egbule ya kara da cewa; yanzu nauyin biyan sabon albashin ya rataya ne a wuyan ofishin akanta janar na kasa.

Ya kara da cewa tin tini dai shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba hannu akan biyan sabon albashi, ya kuma bayyana cewa daga watan Afrilun da shugaba Buhari ya saka hannu, karin N30,000 ta fara aiki don haka daga nan za’a biya kowa.


No comments:

Post a Comment