Pages

Wednesday 21 August 2019

Amurka ta gwada harba makami mai linzami da aka haramta amfani da shi a Duniya

Amurka ta gwada harba makami mai linzami mai cin gajeren zango wanda a shekarun baya Yarjejeniyar Makaman Nukiliya Masu Cin Gajeren Zango ta haramta amfani da shi.


Sanarwar da Ma'aikatar Tsaro ta Amurka Pentagon ta fitar ta ce sun gwada harba makamin sabo wanda ya yi tafiyar sama da kilomita 500.

Rubutacciyar sanarwar da aka fitar daga Pentagon ta kara da cewa "Ma'aikatar Tsaro ta gwada harba makamin mai linzami daga tsibirin San Nicolas dake jihar California. Bayan makamin ya fita ya yi tafiyar kilomita 500 sannan ya sauka a inda a ake so."

Sanarwar ta kara da cewar wannan gwaji zai taimaka a aiyukan da ake yi na samar da makamai masu linzami masu cin gajeren zango.

An gano cewar wannan makami da aka harba ya zama wanda aka haramta amfani da shi a karkashin Yarjejeniyar da aka yi da Rasha a shekarar 1987.

Yarjejeniyar ta INF ta haramtawa Amurka da Rasha harbawa ko amfani da makami mai linzami mai iya tafiyar kilomita 500 da ake harba shi daga kasa. 

A wannan watan ne Ma'aikatar Harkokin Wajen Rasha ta bayyana cewar yarjejeniyar ta INF ta daina aiki.
TRThausa.







Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment