Pages

Wednesday 21 August 2019

Kotu ta bada belin Sirikin Atiku da EFCC ta kama bisa zargin Almundahanar kudi

Sirikin dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP a zaben 2019, Atiku Abubakar watau Abdullabi Babalele da hukumar hana yiwa arzikin kaa zagon kasa ta EFCC ta kama bisa zargin hannu a almundahanar wasu daloli ya shaki iskar 'yanci.



Babbar kotun Gwamnatin tarayya dake Legas ce ta bayar da belin Balele karkashin hukuncin da alkali, Nicolas Owiebo yayi bayan da wanda ake zargi ya ki amincewa da zarge-zargen da ake masa.

Alkalin dai ya bayar da belin Babalele ne akan kudi Naira miliyan 20 sannan kuma da wanda zai tsaya masa wanda kuma dolele ya kasance zaunannen Legas sannan kuma yana da miliyan 20 tashi.

Tun ranar Juma'ar data gabata Babalele ya cika wadannan sharudda na belinshi kuma tuni ya dawo babban birnin tarayya, Abuja.

Saidai wani lauyan Atiku, Uyeikpan Giwa Osagie da dan uwanshi, Erhunse Giwa Osagie da suma hukumar ta EFCC ta kama su bisa zargin hannu a wata almundahanar kudi da suka kai dala miliyan 2 da suma suka ki amincewa da zargin da ake musu sannan kotun ta bayar da belinsu suma akan kudi miliyan 20  kowannensu da wanda zai tsaya musu har yazu suna can a kulle ba'a sakesu ba saboda kasa cika sharuddan belin nasu.





Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment