Pages

Saturday 17 August 2019

Mane ya bada hakuri bayan taimakawa Liverpool ta ci Southampton 2-1

Kungiyar Liverpool ta lallasa Southampton da ci 2-1 a wasan da suka buga a yammacin yau inda Sadio Mane yaci kwallo daya sannan kuma ya baiwa Firmino taimako ya ci kwallo ta biyu.



Bayan kammala wasan Mane ya bayyana cewa, yana baiwa Southampton hakuri kasancewa tsohuwar kungiyarshi ce, kasancewar yanzu ina Liverpool dole incisu kwallo amma ina basu hakuri.

Hakanan wasan da aka buga tsakanin Manchester City da Tottenham shima sun tashi canjaras da sakamakon 2-2, ana gab da za'a tashi wasane dai Gabriel Jesus ya ci kwallo amma daga baya aka kashe ta bayan da alkalin wasa ya duba na'urar nan dake taimakawa alkalin wasa yanke hukunci inda ya gano cewa kwallon ta taba hannun Laporte kamin ta shiga.

Pep Guardiola ya ji haushin wannan abu inda yace ba'a musu adalci ba.

Arsenal ma ta sha da kyar a hannun Burnley inda suka tashi 2-1.

Sai kuma Norwich data lallasa New Castle da ci 3-1.

Aston Villa tasha kashi a hannun Bournemouth da ci 2-1.

Brighton da West Ham sun yu kunne doki 1-1

Sai Everton da taci Watford 1-0






Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment