Pages

Tuesday 20 August 2019

TA HADU DA SHARRIN KAFOFIN SADA ZUMUNTA: Kimanin Kwanaki Biyar Kenan Da Bacewarta

Wannan yarinya sunanta Sadiya daga garin Jos jihar Pilato, ana cikiyarta, ta bata bat yau wajen kwana biyar.


Ta hadu da wani mutum da suka hadu a dandalin sada zumunta, ya mata alkawari zai zo Jos su gana, ta fita daga gidansu akan zata taro bakon nata, to tun daga wannan lokacin ba'a sake jin duriyarta ba

Kuma tun daga lokacin fitar ta daga gida zata taro bakonta nambar wayoyinta duk a kashe, an nemeta sama da kasa an rasa, kuma ba'a san ta inda suka hadu da mutumin ba balle a fara bincike.

A yanzu dai 'yan uwanta sun fitar da neman cigiyarta, jama'a sai a taimaka ko da addu'a.

Daga bangaren mu za mu hada 'yan uwanta da masu bincike a wannan fanni Insha Allah.

Bayan haka 'yan uwa a yi taka tsantsan, wannan darasi ne gare mu gaba daya, a guji saurin yadda da mutane musamman wadanda aka hadu ta kafofin sada zumunta.

Muna rokon Allah Ya bayyanata cikin aminci Amin.

Daga Datti Assalafiy







Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment