Pages

Thursday 22 August 2019

Wata kungiyar kare hakkin bil'adama ta Najeriya ta caccaki Shugaba Buhari kan baiwa musulmai mukaman Minista

Wata kungiyar dake ikirarin kare hakkin bil'adama a Najeriya ta caccaki shugaban kasa, Muhammadu Buhari akan baiwa musulmai mukaman ministocin Tsaro da na harkokin cikin gida.



Kungiyar me suna HURIWA ta hannun shugabanta, Emmanuel Onwubiko da kuma me kula da harkokin watsa labaranta, Zainab Yusuf ta fitar da sanarwa inda ta yi Allah wadai da yanda tace shugaba Buhari na nuna bangaranci wajan rabin mukamai kamar yanda yayi a zangon mulkinshi na farko.

Kungiyar ta yi kira ga shugaba Buhari da yayi kokarin barin tarihi me kyau musamman yanzu da yake zangon mulkinshi na karshe yanda za'a rika tunawa dashi a matsayin shugaban Najeriya ba shugaban wani bangare ba.

Kungiyar tace shugaba Buhari ya kwashe mukaman manyan ministoci ya baiwa 'yan Arewa da Musulmai inda tace kaso 50 cikin 100 na manyan mukaman yankin Arewa maso gabas Buhari ya baiwa amma kuma ya baiwa yankin Inyamurai mukaman kananan ministoci.

Kungiyar tace bata so shugaba Buhari ya maimaita abinda yayi a zangon mulkinshi na farko na baiwa Musulmai kuma 'yan Arewa harkar tsaro inda ya baiwa Arewa ministan tsaro sannan shugaban kula da binciken tsaro da shuwagabannin 'yansanda dana sojoji dana Kwastam dana shige da fice dana frisin dana 'yansandan Farin kaya.

Kungiyar tace muddin ba shugaba Buhari na son rasa kallon da ake mai a matsayin dan kishin kasa ba sannan kuma Uban kasa ya kamata ya canja








Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment