Pages

Sunday 18 August 2019

'Yansanda sun kama wanda suka jefi sanata Ekweremadu a kasar Jamus

A jiyane dai rahotanni daga kasar Jamus suka bayyana yanda wasu inyamurai mazauna kasar Jamu karkashin kungiyarnan dake fafutukar kafa kasar Biafra suka yiwa tsohon mataimakin kakakin majalisar dattijai, Sanata Ike Ekweremadu rotse da cin zarafi a wajan wani taro.




Shugabar hukumar 'yan Najeriya mazauna kasashen waje, Abike Dabiri Erewa ta bayyana rashin jin dadinta ga wannan lamari inda ta yi Allah wadai dashi kamar yanda ta bayyana a shafinta na Twitter.

Tace tana fatan wadanda aka kama zasu fuskanci fushin hukuma akan wannan aika-aika da suka yi.





Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment