Pages

Saturday 19 October 2019

A Karshe Shugaba Buhari Ya Yi Allah Wadai Da Sace Yaran Kano

Alhamdulillah daga karshen al'amari shugaban Kasa Buhari ya jajanta tare da yin Allah wadai da sace yara 9 da wasu Inyamurai sukayi a Kano, aka kaisu Anambra aka canza musu suna da addini aka sayar da su


Shugaba Buhari ya jinjinawa rundinar 'Yan sanda da sukayi kokari wajen gudanar da bincike tare da kubutar da yaran.

Sannan shugaba Buhari yace ba zai taba goyon bayan aikata kowani irin laifi ba har da yin garkuwa da kananun yara

A takaice wannan sanarwan ya fito ne daga Malam Garba Shehu mai magana da yawun shugaban kasa Buhari

Sannan wani abin farin ciki ya faru da Maigirma Kwamishinan 'Yan sanda na jihar Kano, a zaman da shugabannin hukumar kula da aikin 'yan sanda (Police Service Commission) sukayi jiya, daga cikin wadanda aka amince da yiwa karin girma har da Kwamishinan 'Yan sanda na jihar Kano wanda yayi sanadin kubutar da yara tara, zuwa mukamin mataimakin babban Supeta Janar na 'yan sanda AIG

Ina wadanda muka nuna bacin rai saboda shugaba Buhari baiyi magana akan sace yara 9 a Kano ba? da fatan zamuyi hakuri mu karbi uzurin Maigirma shugaban kasa tunda yanzu ya jajanta mana, sai dai muna fata nan gaba idan an cutar da mu a jajanta mana da wuri kamar yadda ake jajantawa Yarbawa da Inyamurai da zaran wani abin jajantawa ya same su

Allah Ka taimaki shugaba Buhari, Ka raba tsakaninsa da maciya amana. Amin.
Datti Assalafy







Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment