Pages

Saturday 19 October 2019

Bana son sakawa Kwantirakin Bugawa Barcelona wasa na har abada>>Messi

Tauraron dan kwallon Barcelona,Lionel Messi ya bayyana cewa bashi da burin sakawa kwantirakin da Barcelonar ta mai ta yi na buga mata kwallo har tsawon rayuwarshi hannu.



Messi ya tabbatar da cewa Barcelonar ta mai ta yin amma yaki amincewa.

Ya bayyana hakane a hirar da yayi da wani gidan rediyin Aregntina me suna Metro 95.1

Messi yace watakila ya bugawa Barca wasa har iya tsawon rayuwarshi amma fa ba wai ta hanyar sakawa kwantiraki hannu ba, yace ya fi son ya ci gaba kamar yanda suke a yanzu.

A kwantirakin da Messi ke bugawa Barca wasa a yanzu, Saura shekaru 2 ya kare




Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment