Pages

Wednesday 16 October 2019

Najeriya Za Ta Fara Amfani Da Jiragen Yaki Marasa Matuka Domin Hana Shige Da Ficen Haramtattun Kayayyaki A Iyakokinta

Shugaban Nijeriya  Muhammadu Buhari ya amince da amfani da jirage marasa matuka da jiragen yaki na musamman da fasahar sararin samaniya domin kiyaye iyakokin Nijeriya, kamar yadda majiyar mu ta labarta mana.


Jaridat 'The Nation' ta ruwaito cewa wata majiya ta ce tsarin yana cikin shirin e-Customs ne da za ayi amfani da shi domin hana shige da ficen haramtattun kayayyaki cikin Nijeriya. 

Bayan an siyo na'urorin da kuma amfani da e-Customs, ana sa ran samun ingantaccen tsaro a kan iyakokin Nijeriya  wadda hakan zai kore bukatar gina katanga Akan iyakokin Nijeriya. 

Majiyar ta ce: "Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari  ya amince da e-Customs. E-Customs ya kunshi amfani da jirage marasa matuka da wasu jiragen sama da kuma amfani da fasahar sararin samaniya domin sanya idanu a kan iyakokin Najeriya domin hana shiga da ficen haramtattun kayayyaki da mutane. Da zarar anyi haka ina tabbatar maka cewa zamu Samu tsaro a iyakokin mu kuma babu bukatar gina katanga.

Wannan na zuwa ne bayan kaddamar da atisayen hadin gwiwa na operation Ex Swift Response. 

Ofishin mai bawa shugaban kasa shawara kan tsaro (ONSA) ce ke jagorantar atisayen da ya kunshi 'yan sandan Nijeriya, Jami'an Kwastam, Immigration, Rundunar sojin Nijeriya da sauran hukumomin tsaro domin magance matsalar tsaro a iyakokin Nijeriya. 

 Shugaban hukumar kula da shiga da ficen mutane, Mohammed Babandede a wurin taron manema labarai a Abuja kan Operation Ex Swift Response ya ce Shugaba Buhari ya amince da aiwatar da dokokin ECOWAS na shige da fice. A cewar dokar idan mutum ba shi da takardun tafiya, Jami'an Immigration ba za su bari ya fice daga Nijeriya ba kuma ba za a bari wadanda ba su da takardun su shigo cikin Nijeriya ba.







Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment