Pages

Saturday 7 December 2019

Abin kunyane yanda Mane ya kare a matsayi na 4 a gasar Ballon d'Or>>Messi

Tauraron dan kwallon kafar Barcelona Lionel Messi da ya lashe kyautar Ballon d'Or ta bana ya bayyana mamakinshi kan yanda dan kwallon Liverpool, Sadio Mane ya zo a matsayi na 4 a waja  bada kyautar ta Ballon d'Or.





Messi ya bayyanawa Canal+ cewa gaskiya abin kunyane yanda Mane ya kare a matsayi na 4 a gasar inda yace shi Mane ya zaba saboda irin nasarar da ya samu a Liverpoo.

Yace saidai matsalar a wannan shekarar akwai 'yan kwallon da suka yi kokari sosai shiyasa zaben gwani guda daya ke da wahala.

Mane ya ciwa Liverpool kwallaye 26  sannan ya bayar da taimako aka ci guda 5 a kakar wasan bara sannan kuma ya taimakawa kungiyar ta lashe gasar Champions League, a bana ma Mane na da kwallaye 13 sannan ya bayar da taimako an ci guda 7.





Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment