Pages

Friday 6 December 2019

Abinda ya faru da Sowore yau a Kotu be taba faruwaba>>Femi Falana: DSS na so su kasheni>>Inji Sowore

Bayan dambarwar da aka sha a kotu a yau yayin da jami'an hukumar 'yansandan farin kaya ta DSS suka farwa shugaban Sahara Reporters inda kasa da awanni 24 bayan da suka sakeshi suka yi yunkurin kamashi bayan da kotu ta dage zaman sauraren shari'ar tashi zuwa shekara me zuwa, Soworen yayi zargin cewa DSS din na son kasheshine.



Ya bayyana hakane ga gidan talabijin na Channels inda yace jami'an DSS sun gaya mai cewa ba zai bar inda suke tsare dadhi da rai ba shine suka zo su tabbatar da hakan a kotu.

Yace amma dolene a samu wanda zasu sadaukar da kansu dan a samu canji a Najeriya.

Shima dai lauya kuma dan rajin kare hakkin bil'adama, Femi Falana dake wakiltar Sowore a kotu ya bayyana cewa be taba ganin wannan abu da ya faru a yau ba na zuwan DSS su kama Sowore a kotu.

Yace DSS sun bayyana cewa suna son yiwa Sowore da abokinshi da aka kamasu tare Olawale Bakare tambayoyine kan wasu sabbin laifukan da suka aikata, yace to ta yaya suka aikata wasu sabbin laifuka inda yace saidai idan a inda DSS din take tsare dasu ne suka aikata laifukan.

Femi Falana da kanshi ya kai Sowore ofishin DSS inda yayi tsammanin su mai tambayoyi saidai daga baya ya bayyana cewa sun sake tsareshi. Yace zasu bi hanyar doka dan gwanin sun kalubalanci wannan sabon kame da akawa Sowore.

Saidai dayan wanda aka kama su tare da Sowore, Olawale Bakare yayi batan dabo inda wani lauya ya bayyana cewa DSS da kansu sun zo har ofishinsu suna neman shi.

Kalli bidiyon yanda aka yi dan barwa kama Soworen a Kotu a kasa:






Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment