Pages

Sunday 8 December 2019

An Kama Matashiya Manajar Banki Ta Bogi A Sokoto

Hukumar dake yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC, dake Sakatariyar Yanki ta Sakkwato, ta kama wata manajar Bankin bogi da laifin karbar kudin jama'a ta barauniyar hanya, mai suna Amina Kabo (wadda aka fi sani da Firdausi Kabo) 


Kamin kamun nata Amina ita ce mai tallata bankin Olive Micro Finance Bank, mara rajista wanda yake a No. 26 Dubabe Plaza a Sakkwato. 

An kama ta ne da laifin aikata laifukan makirci, zagi da kuma karbar kudi ta hanyar karya da makirci na kimanin naira dubu dari takwas da dubu casa'in da dari biyar, (N897,). 

Shugaban yankin, Abdullahi Lawal, yayin da yake gabatar da wadda ake zargin yayin ganawa da manema labarai a Sakkwato ranar Juma’a, 6 ga Disamba, 2019, ya bayyana kamun da cewa “babbar nasara ce”.






Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment