Pages

Saturday 7 December 2019

Madrid Ta lallasa Espanyol da ci 2-0

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta lallasa Espanyol da ci 2-0 a wasan da suka buga na yau na gasar cin kofin La liga inda Benzema da Varane suka ciwa Madrid din kwallayenta.



Benzema na da jimullar kwallaye 11 kenan inda kuma ya bayar da taimako akaci guda 5.

Wasan bai karewa Madrid da dadi ba dan kuwa an baiwa dan wasan bayanta, Ferland Mendy jan kati inda ta kare wasan da 'yan kwallo 10.

Yanzu Madrid na saman teburin La Liga da maki 34 saidai wasan an jima da Barcelona zata yi ne zai tantance ko Madrid zata ci gaba da zama a saman teburin ko kuwa a'a.




Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment