Pages

Wednesday 11 December 2019

Yan Bindiga Sun Sako Jami'in Kwastam Bayan Biyansu Sama Da Naira Milyan Uku A Matsayin Kudin Fansa

Da marecen jiya Talata ne, 'yan bindiga da suka sako jami'in Hukumar Hana Fasa Kwabri nan da suka sace a Karamar Hukumar Dutsinma ta jihar Katsina, Nasiru Ibrahim Dandanko a daren Lahadi.


Majiyar RARIYA ta tabbatar da cewa, 'yan bindigar da suka sace shi, sun kai shi dajin Maidabino da ke Karamar Hukumar Danmusa, inda suka amshi zunzurutun kudi har naira milyan uku da dubu dari tara da hamsi, sannan suka sako shi.

Yanzu haka, Nasiru Ibrahim Dandanko ya dawo cikin iyalansa cikin koshin lafiya Kuma ya ce babu bugu ba zagi a inda suka kai shi. Kuma ya yi godiya ga jama'ar da suka yi masa adduar kubuta daga hannun wadannan yan bindigar.
Rariya.







Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment