Pages

Sunday 26 January 2020

Hotuna: Yanda Biliyoyin Farin dango suka afkawa gonaki a gabashin Afrika

Masana sun yi gargadin cewar, biliyoyin farin dangon dake afkawa gonaki da rumbunan abinci a sassan gabashin nahiyar Afrika, na da nasaba da sauyin yanayi na zafi ko sanyi, zalika barnar farin dangon ka iya sake munana halin farin da wasu sassan gabashin Afrikan ke ciki, la’akari da cewar basu gama farfadowa daga masifun na fari da ambaliyar da suka fuskanta ba.





A makon nan ne dai hukumar bunkasa noma da samar da abinci ta majalisar dinkin duniya FAO ta ce hadarin farin dangon da ya taso daga Habasha da Somalia zuwa Kenya, ya kai girman murabba’in kilomita dubu 2 da 400, kwatankwacin girman birnin Moscow, abinda ke nufin adadin farin zai iya kaiwa biliyan 200.


Hukumar ta FAO ta bayyana mamayar farin dangon a matsayin mafi muni da kasashen Habasha da Somalia suka gani cikin shekaru 25, mafi muni kuma cikin shekaru 70 a kasar Kenya.


Hukumar ta kuma yi gargadin cewar, muddin ba a dauki mataki ba, yawan farin dangon ka iya ninkawa sau 500 nan da zuwa watan Yuni, kuma farin za su bazu zuwa kasashen Uganda da Sudan, abinda zai kai ga tafka hasarar dimbin kayan abinci da sauran amfanin gona.




Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment