Pages

Sunday 26 January 2020

Leah Sharibu ta haifa wa Kwamandan Boko Haram da namiji

Leah Sharibu wacce ita kadai ta rage a hannun kungiyar Boko Haram cikin ‘yan matan makarantar sakandaren Dapci su 110  da ‘yan kungiyar suka yi garkuwa da su a watan Fabrairun shekarar 2018, ta haifar wa daya daga cikin Kwamandojin kungiyar Boko Haram da namiji.


Majiyarmu ta shaida cewa a yau  Asabar Leah Sharibu, ta haihu a kasar Nijar bayan da daya daga cikin Kwamandojin Boko Haram da ke zaune a kasar waje ya aureta.

Majiyar ta ce, a baya bayan nan kungiyar ta Boko Haram tayi yunkurin sakin Leah Sharibu, sai dai ta fasa yin hakan ne sakamakon tsohon cikin da yarinyar ke dauke da shi.

An yi garkuwa da ita ne a lokacin da take da shekara 14, inda ‘yan kungiyar suka ki sakinta bayan sun saki ‘yan uwanta daliban da suka yi garkuwar dasu, an bayyana cewa sun ki sakin Leah Sharibu ne saboda ta ki barin addininta na Kiristanci ta koma Musulunci.







Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment