Pages

Friday 24 January 2020

Kwankwaso na son komawa APC dan tsayawa takarar shugaban kasa a 2023

Gwamnan Kano, Dr. Umar Abdullahi Ganduje ya bayyana cewa tsohon gwamnan jihar, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na shirin komawa jam'iyyar APC dan yayi takarar shugaban kasa a shekarar 2023.




Ganduje ya bayyana hakane a yayin da yake karbar dandazon 'yan jam'iyyar PDP da suka koma APC, yace yasan duk wata dabara irin ta kwankwaso a siyasance mutum ne wanda be da alqibla kuma komai dan kanshi yake yi sannan duk abinda zaka mai bazai gode maka ba.

Ya kara da cewa koda a shekarar 1999 da suka yi takara tare Kwankwaso baici zaben fidda gwani ba, Gandujenne yaci amma aka sasantasu. Yace kuma shi ogan Kwankwaso ne dan a lokacin shine ya dauki nauyin yiwa Kwankwason fastocin yakin Neman zabe kuma ya tattaro mai magiya baya daga duka kananan hukumomin Kano 44.




Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment