Pages

Saturday 25 January 2020

Shugabar matan Kannywood ta kare matan masana'antar dake Fita kasashen Waje

SHUGABAR Ƙungiyar Matan Kannywood ta masu shirya finafinan Hausa ('Kannywood Women Association of Nigeria', K-WAN), Hajiya Hauwa A. Bello, ta kare 'yan'uwan ta jarumai mata waɗanda ke karakaina a ƙasashen ƙetare.


Ta ce kallon da ake yi masu ba haka ba ne.

Hauwa ta na magana ne a kan wani rahoto da mujallar Fim ta buga a makon jiya mai taken "Ina Matan Kannywood Ke Samun Kuɗi Su Na Zarya A Ƙasashen Waje?"

A rahoton, mujallar ta yi labarin yadda ake ganin wasu ƙalilan daga cikin fitattun jarumai mata su na yawace-yawace a ƙasashen waje da sunan yawon buɗe ido ko zuwa Umrah, inda ta yi ayar tambaya kan inda su ke samo maƙudan kuɗaɗen da su ke kashewa a tafiye-tafiyen bayan kuma yanzu ba fim su ke sosai ba.

Irin waɗannan jaruman sun haɗa da Hadiza Gabon, Rahama Sadau, Nafisat Abdullahi, Fati Washa, Sapna Aliyu Maru, da ma wasu.

A cikin 2019 kaɗai an ga wata ko wasun su a ƙasashe da su ka haɗa da Amurka, Ingila, Faransa, Cyprus, Indiya, Dubai, Saudiyya, Ethiopia, Spain, Masar, da sauran su. 

Hakan na faruwa ne a daidai lokacin da harkar fim ba ta ci saboda lalacewar kasuwa, babu mai samun wani abin a zo a gani.

A martanin da ta turo wa mujallar, Hauwa A. Bello ta ce, "Su na da hanyoyin samun kuɗi duk da cewar a yanzu harkar kasuwar finafinai ta na cikin wani yanayi na durƙushewa, a sakamakon halin da ƙasar ta ke ciki."

Ta ce ba shakka ba daga harkar fim jaruman ke samun manyan kuɗaɗe ba.

Shugabar, wadda aka fi sani da Hauwa Edita, ta ce waɗannan jaruman su na samun talla daga manyan kamfanoni, kuma an koyar da su yadda za su caji maƙudan kuɗi a kan kowace talla.

Ta yi nuni da cewa kamar Hadiza Gabon da aka bada misali da ita, ai ta na tallar kamfanoni irin na su Ɗangote, ta ce, "To nawa ta ke samu a wannan tallar?" 

Haka kuma ta ce 'yan fim ɗin sun yi tallar 'yan siyasa a zaɓen da aka yi bara, don haka idan sun je yawon shaƙatawa ai don su na samun kuɗin ne.

Ta ƙara da cewa, "Ko da aka ce su na yawan fita, to sau nawa su ke fita ɗin? Ai ba ko da yaushe su ke tafiyar ba; wasu ma sai shekara-shekara su ke zuwa."




Haka kuma ta ce ya kamata Fim ta tambaye su inda su ke samun kuɗin, ba kawai ta rubuta labari a kan su ba, "domin na san duk wacce aka samu ana so a yi hira da ita babu wacce za ta ƙi."

Sai dai kuma kamar yadda labarin ya nuna, wakilan mujallar sun tuntuɓi wasu daga cikin waɗannan jaruman kan lamarin, amma su ka ƙi magana in ban da Sapna wadda ta ce ita da ma ta saba zuwa Dubai saro kayan da ta ke sayarwa a shagon ta.

Hauwa Edita ta ce, "Mata su na son idan sun samu kuɗi su ji daɗi, su killace kan su, to shi ne su ma 'yan fim ɗin su ke tafiya su zagaya duniya.

"Kamar sauran mutane ne, su na son su ji daɗi, don haka tun da Allah ya riga ya ɗaukaka su su na da wajen da za su samu kuɗi."

Sannan a kan zargin da wani ya yi a cikin labarin mujallar cewa matan kan samu kuɗi ne a wajen maza, Hauwa ta ce, "Kowa ya san mace a wajen namiji ta ke samun kuɗi, to haka ma su 'yan fim mata a wajen maza su ke samun kuɗin su."

Sai dai ta ce maza kan yi wa matan hanyar samun kwangilar talla, ba kamar yadda ake tunani ba.

Ta ce: "Kuma akwai abubuwa da dama da za a yi a samu kuɗi, ba sai an yi fim ba. Kamar mu ƙungiyar mu ta Matan Kannywood akwai hanyoyi da dama da mu ka bijiro da su na talla da sauran su."




Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment