Pages

Saturday 25 January 2020

'Ya kamata a yi amfani da maniyyin mazan da suka mutu'

Wani bincike da aka gudanar ya ce ya kamata a rika karbar gudummawar maniyyin mazan da suka mutu.


Binciken wanda aka wallafa a wata mujalla ta Journal of Medical Ethics ya ce yin hakan zai bayar da dama don kara yawan maniyyin da ake da shi a ajiye.

A shekarar 2017 a Birtaniya, an haifi jarirai 2,345 bayan bayar da gudummawar maniyyin.



Amma ana samun karancin gudummawar maniyyi a kasar saboda tsauraran dokoki.

Za a iya daukar maniyyin mutum bayan mutuwarsa ko dai ta hanyar yin amfani da hanyoyi na zamani ko kuma yin tiyata, sannan kuma za a iya daskararwa.

Bayanai sun ce maniyyin da aka samu daga mazan da suka mutu na iya sanya mace ta samu juna biyu da kuma haifar lafiyayyun yara ko da an debi maniyyin ne kwana biyu bayan mutum ya mutu.


A rahoton, Dakta Nathan Hodson, na jami'ar Leicester da Dakta Joshua Parker daga asibitin Wythenshawe da ke Manchester sun ce yin amfani da wannan hanya dai-dai yake da bada gudummawar wani sashi na jikin dan adam.

"Tun da mutane suke iya bayar da gudummawar wani sashi na jikinsu domin a yi dashe don kubutar da rayuwar mara lafiya, ba mu ga wani dalili da zai sa ba za a fadada abin ba ga sauran matsaloli na rashin haihuwa." a cewarsu.

Sai dai, batun zai janyo tambayoyi game da samun izinin iyali kuma akwai damuwa kan batun boye ainihin wanda ya bayar da gudummawar, in ji su.


A 2014, Birtaniya ta bude wani kundin adana maniyyi a Birmingham tare da tallafin £77,000 daga gwamnati.

Bayan kasa da shekara biyu ne aka rufe kundin aka kuma daina karbar gudummawar maniyyi.

Tun 2005, dokar ta ce dole ne masu bayar da gudummawar maniyyi a Birtaniya su amince cewa duk wani yaro da aka haifa ta wannan hanya zai iya tuntubar su idan suka cika shekara 18.
BBChausa.







Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment