Pages

Tuesday 21 January 2020

Yadda Ake Sanyawa Jarirai Sunan Gwamna Badaru A Jigawa

Mataimakin shugaban majalisar kansilolin karamar hukumar Gumel, Hon. Halilu Mohammad ya radawa jaririnsa sunan Gwamnan jihar Alhaji Muhammad Badaru Abubakar, kamar yadda ya alkawarta.


Ya bayyana cewa tun lokacin da matarsa ta samu juna biyu, yake addu'ar Allah ya ba shi da namiji domin ya sanya masa sunan Badaru.

Ya ce ya yi hakan ne saboda adalcin Gwamnan jihar su, nutsuwar sa, rashin girman kai, girmama manya, daraja dan Adam da Kuma uwa uba riko da addini.

A karshe ya yi addu'ar Allah ya sa jaririn sa ya tasirantu da kyawawan dabi'un wanda ya ci sunan nasa.

An yi addu'ar radin sunan jaririn ne a ranar Lahadi, 19 / 01 / 2020, a babban masallacin Juma'a na fadar Mai Martaba Sarkin Gumel.

Rahotanni sun nuna cewa ba wannan ne karo na farko da ake radawa sabbin jarirai sunan gwamna Badaru ba a jihar Jigawa.







Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment