Pages

Monday 27 January 2020

Yahaya Ya mutu Yana tsaka da lalata da Victory Amaize

Wani mutum mai suna Danjuma Yahaya Ali ya mutu yayin da yake tsaka lalata da wata mata me suna Miss Victory Amaize a shahararren Hotal din da ake Wuse 5 babban birnin tarayya Abuja da ake kira da Ibro Hotel.



Matar na fuskantar zargin kisa ta hanyar yin jima'i me yawa da Yahaya wanda ya kaishi ga har ya rasa ranasa inda yanzu haka take hannun 'yansanda kamin a kammala Bincike.

Ranar 22 ga watan Janairunnanne me kula da hotal din ya kaiwa jami'an yansanda korafin cewa Yahaya ya Mutu yayin da yake tare da Victory. Ya bayyana cewa sun iskeshi kwance yana nishi sama-sama inda suka yi gaggawar kaishi Asibiti amma Likita ya tabbatar da cewa ya mutu.

Victory dake zaune a Life Camp, Babban birnin tarayya, Abuja ta bayyana cewa suna cikin Lalatane kawai sai taga ya fara sukewa yana nishi sama-sama sai ya fadi ya mutu.

An dai ajiye gawar Yahaya a Mutuware inda Likitoci zasu yi bincike akanta dan gano ko Victory ta jashi sun yi lalata ta tsawon lokaci da hakan yayi sanadiyyar mutuwarshi, idan hakan ya tabbata to zata iya fuskantar hukuncin daurin shekaru da yawa a Gidan Yari, kamar yanda PM Express ta ruwaito.





Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment