Pages

Saturday 25 January 2020

Zan so a yi adalci wajen sauya mulki a 2023>Shekarau

Tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau kuma dan majalisar dattawa a jam'iyyar APC a Najeriya ya ce zai so ya ga an yi adalci idan aka zo mika mulkin shugabancin Najeriya a 2023.


Shekarau ya bayyana cewa ra'ayinsa kan wanda zai gaji Shugaba Muhammadu Buhari shi ne a duba a yi adalci a kowane bangare da ya dace ya mulki kasar.

A hirarsa da BBC, ya ce "a jam'iyyarmu ta APC ya kamata mu zauna mu tattauna mu ga mene ne zai zama adalci ga ko wane bangare a Najeriya."

Ya ce "tsarin adalci shi ne idan wani bangare ya yi a bai wa wani bangaren dama shi ma ya yi, don a samu zaman lafiya."



Ibrahim Shekarau ya ce akwai rarrabuwar kawuna a jam'iyyar APC a yanzu, inda wasu ke ganin bai dace a bai wa bangaren Kudancin Najeriya ya yi mulki bayan Shugaba Buhari da ya fito daga Arewaci ba, yayin da wasu ke ganin bangaren kudu ne ya kamata a ba dama.

"A daina tursasawa, don ka ga kana da yawa kullum ka ce kai ba za ka saurari kowa ba yawan ka ya ishe ka, a daina kama karya a jam'iyya, a rika sauraren hujjoji," a cewarsa.

"Ko mutum daya ne ya daga hannu ya ce yana da hujja to sai a saurare shi," a cewar Sanata Shekarau.

Ya ce abin da ya fi dacewa shi ne a zauna a teburi a yi shawara yadda kowa zai bijiro da dalilansa sannan a yanke shawarar yadda za a tafi da kowa a mulkin kasar.

"Ko a addini an ce a dinga kallon maslaha, mene ne zai haifar da samun yarda a tsakanin al'umma kuma mene ne zaman lafiya? Haka ne za a samar da natsuwa a kafa gwamnati," a cewarsa.

Ya ce idan aka yi duba abubuwan da suka faru a shekarar 1999, jam'iyyun siyasa a lokacin sun gamsu cewa an yi wa yankin Kudu maso Yamma rashin adalci a zaben 12 ga watan Yunin 1993.

"Shi ya sa aka amince duka 'yan takarar shugabancin kasar na manyan jam'iyyu na wancan lokacin 'su fito daga yankin."





Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment