Pages

Friday 14 February 2020

'Farin jinin Buhari yana raguwa a tsakanin talakawa'

Wani mai sharhi a kan harkokin yau da kullum, Kole Shettima, ya ce tura ce ta fara kai wa bango shi a sa al'umar jihar suka yi wa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ihu lokacin da ya kai ziyara jihar.


Ranar Laraba wasu al'umar jihar suka yi wa shugaban ihu lokacin da ya kai ziyarar jaje kwanaki kadan bayan harin da wadanda ake zargi 'yan Boko Haram ne sun kai a garin Auno, lamarin da ya yi sanadin mutuwar akalla mutum 30.

Harin ya taba ran wasu 'yan jihar, ciki har da Gwamna Babagana Zulum da tsohon gwamna Sanata Kashim Shettima da dan majalisar dattawa, Mohammed Ali Ndume.

Dukkansu sun yi kira a sake salon yaki da kungiyar Boko Haram, wacce ta shafe fiye da shekara goma tana kai hare-hare a arewa maso gabashin Najeriya.

Zai ci gaba da samun matsala

A hirarsa da BBC, Dr SKole Shettima ya ce hare-haren da ake ci gaba da kai wa Borno musamman al'amarin da ya faru a a kwanan nan da kuma yadda aka tarbi shugaban kasa a Maiduguri sun nuna cewa farin jininsa ya fara raguwa a wajen talakawa.

"An fara kai wa halin da talakawa suke ganin abin da suke tsammani basu samu ba, musamman rashin zaman lafiya da ake samu daga hare-haren Boko Haram.

"A siyasance idan har Buhari bai gyara abubuwan da ke damun talakawa ba, farin jininsa zai ci gaba da raguwa," in ji shi.




Shettima na ganin duk da cewa Buhari ya ba mutanen Borno manyan mukamai na tsaro, amma sun gaza shawo kan matsalar, wadanda kuma ya kamata ya sauya.

"Idan bai tashi ya saurari bukatun talakawa ba abin da [na kusa da shi] suke fada masa ba, to abubuwan da suka faru kamar ihun da aka yi masa zai ci gaba. Zai ci gaba da samun matsala tsakaninsa da talakawansa"

Borno dai na daga cikin jihohin da shugaban kasar yake da gagarumin goyon bayan jama'a, don haka mutane da dama ke cike da mamaki kan wannan nuna fushi.




Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment