Pages

Tuesday 11 February 2020

Kaso 87 cikin 100 na talakawan Najeriya na Arewa>>Bankin Duniya

Wani sabon Rahoto da bankin Duniya ya fitar ya bayyana cewa kaso 87 cikin 100 na talaucin da Najeriya ke fama dashi yana yankin Arewa ne.



Rahoton ya fitar da sakamakon binciken da aka yi ne a shekarar 2016 inda yace kuma a Yankin Arewar ma yankin Arewa Maso yamma ne ke dauki da rabin wadannan talakawa

Talaucin ya fi yawa a Kauyuka inda mutane ke rayuwa kasa da layin talauci na Duniya.

Rahoton yace matsalolin ta'addanci, Rashin Tsaro, Rashin Ilimi na daga cikin abubuwan da ke taka rawa wajan kara Talauci a Najeriya wadda Rahoton yace Arewar na da talakawa Fitik da suka fi na ko ina a Duniya fama da tsananin Talauci.

Rahoton yace tsare-tsaren gwamnati na kawo sauki da tallafawa mutane dan rage radadin Talauci basu taka wata rawar azo a gani ba wajan rage talauci a yankin Arewa ba.

Rahoton ya bayyana cewa Ambaliyar ruwa ma da canjin yanayi sun taimaka wajan kara yawan talakawa a Arewa inda jama'a da yawa suka bar gidajensu saboda irin wadancan ibtila'i daya fada musu.

Rahoton ya kuma bayyana matasalar Boko Haram inda yace mafi yawancin wanda Kungiyar take dauka aiki basu da ayikin yine sannan kuma basu iya wata sana'a ta neman na kansu ba wanda hakan ke sawa cikin sauki ake canja musu ra'ayi.

A watan ranar 28 ga watan Janairu na shekarar 2020 nan ne aka fitar da Rahoton wanda yace Rabin talakawan Najeriyar suna yankin Arewa Maso Yammane. Kididdigar hukumar dake kula da mutanen da suka rasa muhallanci suke zaman gudun hijira sun kai sama da miliyan 2 a Najeria a shekarar 2018, kamar yanda Jaridar Punch ta ruwaito.





Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment