Pages

Tuesday 2 January 2024

Sunayen Allah (99) Tare Da Fa’idar Kowane Suna Da Kuma Yadda Za A Yi Amfani Da Shi



KARANTA KA KARU
Huwaallahul ladhii laa ilaaha illaa huwa.
Da sunan Allah mai Rahama Mai Jin kai.
 
Sunnar ma'aiki, Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam ta sanardamu cewa duk wanda ya haddace kyawawan sunayen Allah madaukakin sarki zai shiga Aljannah.
 
Bukhari da Muslim sun ruwaito daga Abu Huraira cewa, Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam yace, Allah na da sunaye 99, duk wanda ya haddacesu zai shiga Aljannah.
Hadisin sama na dauke da abubuwa 3:
Haddace sunayen Allah.
Da kuma fahimtar ma'anarsu.
Da aiki da abinda suka kunsa.
To idan mutum yasan Allah daya ne, ba zai hadashi da kowa ba wajan bauta.
Idan mutum yasan Allah ne me bayarwa, ba zai nema wajan wanin Allah ba.
Idan mutum yasan Allah me Rahama ne, zai aikata ayyukan da zasu sa ya samu rahamar Allah, da dai sauransu.
 
Hakanan kuma ana son mutum ya rika kiran Allah da wadannan sunaye nasa.
 
Kamar yanda Allah madaukaki ke cewa, "kuma dukkan sunaye mafiya kyawu sun tabbata ga Allah, dan haka ku rika kiransa da su [al-A‘raaf 7:180]
 
Misali mutum zai iya cewa, ya mai Rahama ka min Rahama, Ya me Gafara, kamin gafarar zunubaina, da dai sauransu.
 
Dan haka ba haddacewa kadai ya kamata ayi ba, a haddace, a san ma'anarsu, a rika amfani da sakon da suke dauke dashi, a kuma rika kiran Allah da wadannan sunaye.
 
Allahu (Sunane na ubangiji)
shin ne madaukaki acikin sunayensa. Yana daga fa'idar sa idan mutum ya karanta shi sau dubu (1000) Allah zai bashi lafiya ga kowane irin ciwo da ya dame shi.
 
1. ARRAHMANU.
 
(Sarki mai ba kowa da kowa)
Yana daga fa'idar sa wanda ya karanta (100) bayan kowace Sallar farilla ubangiji zai kiyaye shi ga barin rabkana da kuma samun fahimta.
 
2. ARRAHIMU.
 
(Mai jinkan muminai).
Yana daga fa'idarsa wanda ya karanta shi sau (100) ubangiji zai saki ga66ansa wajen yin ibada.
 
3. AL-MALIKU.
 
(Mai gyara bayinsa)
Fa'idarsa a karanta shi sau (100) bayan rana tayi zawali domin samun tsarki a zuciya da samun wadata.
 
4. AL-KUDDUSU
 
( Tsarkakakke ga barin tawaya).
Ana karanta shi sau (100) Allah zai kar6i ibadar wanda ya karanta shi kuma zai yarda da shi.
 
5. ASSALAMU
 
(Mai shigar da bayinsa muminai aljanna).
A karanta shi sau (121) ga mara lafiya. Allah zai bashi lafiya nan take da izinin Allah.
 
6. AL-MUMINU
 
(Mai bawa annabawa mu'ujiza)
Wanda ya karanta shi sau (36) Allah zai aminta da shi daga dukkan abin tsoro.
 
7. AL-MUHAIMINU
 
(Mai tsinkayar ayyukan halitta).
Wanda ya karanta shi sau (100) Allah zai kame ga66ansa ga barin sa6o.
 
8. AL-AZIIZU
 
(Mai girman alkadari).
Wanda ya karanta shi sau (40) kwana (40) a jere, Allah zai wadata shi ga barin rokon halittarsa.
 
9. AL-JABBAARU
 
(Mai gyara bayinsa)
Wanda yake karanta shi a kowace safiya sau (226) ubangiji zai bashi rinjaye ga dukkan azzalumai.
 
10. AL-MUTAKABBIRU
 
(Tsarkakakken sarko).
Wanda ya shi sau (10) yayin da zai sadu da iyalinsa Allah zai azurta shi da 'da namiji.
 
11. AL-KHAALIKU
 
(mai samar da halitta)
wanda ya karanta shi sau (100) a tsakiyar dare Allah zai haskaka zuciyarsa zai ya bashi kwarjini a fuska.
 
 AL-BARI'U
 
12. (mahalicci)
Yana daga fa'idarsa a karanta sau (100) kullum har kwana (7) Allah zai kiyaye wanda ya karanta daga dukkan cutuka masu wuyar magani.
 
13. AL-MUSAWWIRU
 
(mai kyautata halittar bayinsa)
wanda ya karanta sau (21) a kullum Allah zai bashi hikima cikin sana'arsa.
 
14. AL-GAFFARU.
 
(Mai suturce zunuban bayinsa)
Wanda ya karanta shi sau (100) bayan sallar juma'a alamomin albarka za su lullu6e shi.
 
15. AL-KAHHARU
 
(Mai baiwa).
Wanda ya yawaita karanta shi ubangiji zai bashi kwarjini wurin al'umma.
 
16. AL-WAHHABU
 
(Mai karya makiyan addininsa).
Wanda ya yawaita karanta shi Allah zai azurta shi da hakuri da kadan
 
17. AR-RAZZAKU
 
(mai shimida baiwarsa)
Fa'idarsa wanda yake karanta shi sau (10) kullum bayan sallar asubahi zai samu biyan bukatarsa cikin gaggawa.
 
18. AL-FATTAHU.
 
(Mai bude kofofin fake).
Wanda yake karanta shi sau (71) a kullum Allah zai bashi hasken zuciya.
 
19. AL-ALIMU
 
(Masanin komai) Yana daga
fa idarsa samun ilimi da sanin ubangiji.
 
20. AL-KABIDU
 
(mai damke arzikin wanda yaso)
Wanda ya rubuta shi sau (4) har kwana (40) Allah zai kiyaye shi daga ciwon ciki.
 
21. AL-BASIDU
 
(Mai ciyar da bayinsa)
wanda ya karanta sau (10) bayan sallar walha ubangiji zai bude masa kofofin wadata.
 
22. AL-KHAFIDU
 
(mai kunyata makiyan addininsa)
wanda ya karanta shi sau (500) Allah zai isar masa da duk abinda ya dame shi.
 
23. AR-RAFI'U
 
(Mai daukaka waliyansa)
Wanda yake karanta shi sau (70) Allah zai kiyaye shi daga zaluncin azzalumai.
 
24. AL-MU'IZZU.
 
(Mai bada mulki).
Wanda yake karanta shi sau (40) a kullum Allah zai bashi kwarjini.
 
25. AL-MUZILLU
 
(Mai ta6ar da azzalumai)
Wanda ya karanta shi sau (75) Allah zai ku6utar dashi daga dukkan hadari.
 
26. AS-SAMI'U
 
(Maji rokon bayinsa).
Wanda ya karanta ranar juma'a bayan sallar walha zai zamo mujabu da'awati.
 
27. AL-BASIRU
 
(Mai ganin bayinsa)
Wanda ya karanta ranar juma'a sau (100) Ubangiji zai bashi basira.
 
28. AL-HAKAMU
 
(Wanda ba'a juyar da hukuncinsa)
Wanda ya karanta shi a karshen dare a bisa tsarki Allah zai kyautata badininsa sa zahirinsa.
 
29. AL-ADALU
 
(Ya tsarkaka ga barin zalinci)
Wanda ya rubuta ranar juma'ah ko daren juma'ah sau (20) Allah zai hore masa dukkan halitta.
30. AL-LADIFU
(masanin boyayyen lamari)
Wanda ya karanta shi sau (133) Allah zai yalwata arzikinsa.
31. AL-KHABIRU
(Babu abinda yake 6uya ga halittarsa)
Wanda ya karanta sho sau (7) kwana (7) Allah zai ku6utar da shi daga wanda yake tsare da shi.
32. AL-HALIMU
(Mai rangwame)
Wanda ya rubuta shi a takarda ya wanke da ruwa ya shafa kayan sana'arsa zai samu albarka a cinikinsa.
33. AL-AZIMU
(mai girman kadari)
Wanda ya karanta shi a kullum sau (12) Allah zai kiyaye shi daga dukkan abin ki
34. AL-GAFURU
(Mai sitirce bayinsa).
Wanda ya rubuta shi ya shayar da shi ga wanda hauka ya same shi zai warke nan take da yardar Ubangiji.
35. ASH-SHAKURU
(Mai bada lada).
Wanda ya rubuta shi ya shayar da da shi ga mai jiki zai samu saukin jikinsa.
36. AL-ALIYU.
(Mai isa matuka).
Wanda ya rubuta shi ya shayar da shi ga yaro karami Allah zai raya wannan yaron ya kai har girmansa
37. AL-KABIRU.
Mai girman sha'ani)
Wanda ya karanta shi kullum sau (1000) Ubangiji zai maida shi akan mulkinsa
38. AL-HAFIZU.
(Mai isa matuka) wanda ya karanta shi a wurin da yake jin tsoro Allah zai kubutar dashi
39. AL-MUKITU.
(mahaliccin abinci).
Wanda ya karanta shi akan tur6aya kuma ya shaki turbayar zai samu rimjaye a dukkan lamarinsa.
40. AL-HASIBU.
(Mai baiwa bayinsa).
Wanda ya karanta shi sau (27) zai rinjayi makiyansa.
41. AL-JALILU.
(Mai girma akan komai).
Wanda ya karanta shi zai samu kwarjini a cikin jama'a.
42. AL-KARIMU.
(Mai baiwa).
Wanda ya karanta shi lokacin da zai kwanta Allah zai sanya shi cikin waliyyansa.
43. AR-RAKIBU.
(Mai tsinkayarayyukan bayi).
Wanda ya karanta shi ga mai nakuda sau (7) zata haihu da gaggawa da izinin Allah.
44. AL-MUJIBU.
(Mai amsa rokon bayinsa).
Wanda ya karanta shi a kullum Allah amsa rokonsa.
45. AL-WASI'U.
(Masanin komai).
Wanda ya karanta shi Ubangiji zai kiyaye shi da yin hako ga bayin Allah.
46. AL-HAKIMU.
(Mai isa cikin hikima).
Wanda yake yawan karanta shi Allah zai bude masa kofofin hikima.
47. AL-WADUDU
(Masoyin muminai)
Wanda ya karanta shi sau (1000) zai sai soyayyar ubangiji (S.W.T)
48. AL-MAJIDU
(Mai cikakkiyar sifa).
Wanda ya karanta shi yayin 6ude baki Allah zai kiyaye shi ciwon albaras.
49. AL- BA'ISU
(Mai aiko manzanni)
Wanda ya karanta yayin da zai kwanta sau (100) Allah zai bashi hasken ilimi.
50. ASH-SHAHIDU.
(Masanin dukkan komai).
Wanda ya karanta shi a kowane lokaci Allah zai tabbatar da shi akan gaskiya.
51. AL-HAKKU.
(Matabbacin samuwa).
Wanda ya karanta shi Allah zai sanya arziki a hannunsa
Rariya.

 

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment