Pages

Wednesday 17 May 2017

Zannah Mustafa: Gwarzon lauyan daya jagoranci sakin 'yan matan chibok


A jerin wasikun da muka samu daga 'yan Jaridu da dama da marubuta daga Afirka, Marubuciya Adaobi Tricia Nwaubani ta samu tattaunawa da Lauyan da ya taimaka wajen shiga tsakanin gwamnati da mayakan Boko Haram, wajen sako 'yan matan Chibok 82.

A lokacin da Zannah Mustapha mai shekara 57 ya je wajen da za a mika 'yan matan 82 da kungiyar Boko Haram ta sako bayan shafe shekara uku a hannunta, wani dan kungiyar ne ya yi ta kiran sunayen 'yan matan.

Daya bayan daya, 'yan matan suka yi layi a wani daji da ke kusa da garin Kumshe, da ke kan iyakar Najeriya da Kamaru, ko wacce sanye da bakin dogon hijabi daga sama har kasa.



"Na je tare da kungiyar Red Cross. Kuma sun kowa min 'yan matan, "In ji Mustapha, wani lauya a jahar ta Borno da ke arewa maso gabashin kasar.


Ya yi ta kokarin shiga sasantawa tsakanin gwamnati da mayakan kungiyar wajen sakin 'yan matan tare da kawo karshe hare-haren da kungiyar ke kai wa a kasar.

A shekarar 2015, shugaba Buhari ya fada wa kafafen yada labarai cewa gwamanatinsa a shirye take wajen tattaunawa da "sahihan" shugabannin kungiyar domin ganin an sakon 'yan matan.

Fiye da 'yan mata 200 ne dai kungiyar ta kama a shekara 2014 a makarantar Chibok da ke arewa maso gabashin kasar, lamarin da ya tayar da hankalin duniya.

An yunkurin yin sulhu sau da dama a baya amma ba a samu nasara ba, saboda yadda bangarori daban-daban suka dinga fitowa daga kungiyar suna ikirarin cewa suke da iko da 'yan matan.

Lauya Mustapha ne ya yi nasarar jawo hankalin gwamnati da cewa wannan kungiya a dauke ta a yadda ta ce, in ji mai magana da yawun shugaban kasa.


Ya ce, "Ya sha tattaunawa da su a baya, kuma sun cika alkawarinsu."

Kokarin da Mustapha ya yi na shiga tsakani, ya samo asali ne tun shekarar 2007 lokacin da ya samar da wata makarantar addini ga yara marayu da marasa galihu domin ilimantar da su addini kyauta.

Lokacin da rikicin Boko Haram ya yi kamari a 2009, makarantar ta rika daukar yaran sojoji da jami'an gwamnati da kungiyar ta halaka iyayensu, da kuma 'ya'yan 'yan kungiyar da gwamnati ta kashe iyayensu.


Daga nan sai Mustapha ya nemi taimakon kungiyar agaji ta Red Cross, domin ciyar da daliban makarantar tasa kyauta.

Ya kuma karfafa wa iyaye gwiwa da su kafa wata kungiya, da za ta kai ga matan da mazansu suka rasu, domin jawo hankulansu da su tura 'ya'yansu zuwa makarantar.
Daga baya sai Red Cross ta kara fadada ayyukanta na agaji, ga sauran iyaye mata, inda take ba su abinci da sauran kayayyaki kyauta ko wanne wata.

"Wannan kuwa ya faru ne lokacin da aka kama matan mayakan tare da rusa gidajensu, don haka sai Kungiyar Boko Haram, ta rika kallona tare da Red Cross a matsayin 'yan ba ruwanmu." in ji mustapha.

Lokacin mulkin Jonathan, Obasanjo ya kai ziyara Maiduguri cibiyar kungiyar, don shiga tsakani wajen kawo karshen rikicin.

Ya kafa wani kwamiti, domin tattaunawa da kungiyar don kawo zaman lafiya. Mustapha na cikin wannan kwamitin saboda kyakkyawar alakar da yake da ita da iyalan mayakan kungiyar.

Bayan da Jakadan kasar Swizland a Najeriya ya kai ziyara zuwa makarantar Mustapha a 2012, ya shirya wa Mustapha tafiya zuwa biranen Zurich da Geneva domin samun kwarewa a aikin shiga tsakani.

Mustapha ya ce "Muna kokarin shiga tsakani da kungiyar domin samar da zaman lafiya, tun kafin a sace 'yan matan Chibok,"

Tattaunawar shiga tsakaninmu ta farko, ita ce ta sakin 'yan matan Chibok 20 a farko.
Amma, saboda yadda yake da kyakkyawar alaka da kungiyar, sai ta kara masa yarinya daya, wadda Mustapha ya ce kyauta ce a gare shi, da kungiyar ta yi masa, wanda ya sa 'yan matan suka zama 21.


Lokacin da aka sake su a watan Oktobar 2016, an zabe ta, da ta karanto sunayen sauran 'yan matan 20 da za a saka.

Mustapha ya ce mayakan sun jera 'yan matan 21, kuma suka tambaye su da cewa ko sun taba yi musu fyade? Sai gaba dayansu suka ce ba su taba ba.

Lokacin da mayakan suka tambayi wata da jariri ke kuka a hanunta, sai ta ce tana da ciki lokacin da aka sace su, saboda ta yi aure makonni kafin a sace su.

Ta ce jaririyar da ke hannunta, 'yar mijinta ce.

Kungiyar Boko Haram ta ce tana so mutane su san cewa, sai idan 'yan matan sun "amince" sun auri 'yan kungiyar ne kawai suke saduwa da su.

Lokacin da za a saki wadannan 'yan mata 82 a farkon watan Mayu, an kara jera su aka tambaye su irin tambayar da aka yi wa 21 na farko.

Daya daga cikin kwamandojin kungiyar bakwai da ke tare da su, ya tambaye su daya bayan daya: "A iya tsawon zaman da kuka yi tare da mu, an taba yi wa daya daga cikinku fyade ko aka taba jikinta? Sai dukkansu suka ce ba a taba ba," In ji Mustapha.

Babu daya daga cikin rukuni na biyu na 'yan mata 82 da ta zo da yaro.

Sai dai daya daga cikinsu na da karaya a kafarta, kuma tana tafiya da karafa, raunin da aka ce wa Mustapha ta samu ne sakamakon harin da sojojin kasar suka kai wa kungiyar ta sama.


Duk sun ruga da gudu'

Bayan an kammala kiran sunayen 'yan matan 82 sai Mustapha ya sanar da su cewa, "yau kun kubuta"

"Sai duk suka yi murmushi," in ji shi.

Ya yi amanna cewa, sun kasa bayyana murnarsu a fili ne, saboda kwamandojin kungiyar da ke wajen, wadanda ke dauke da bindigogi, wasu ma sanye da kaya da takalman sojoji.

Sai Mustapha ya dauki hotuna da 'yan matan. Su kuma kwamandojin kungiyar suka nadi bidiyon abin da yake faruwa. Sai kuma motacin Red Cross suka karaso wajen.

"Da na ce musu su tafi su shigo motacin, sai gaba dayansu suka ruga da gudu," in ji shi.
"Suna shiga motocin, sai suka fara rera wakokin murna. Wasu na zubar da hawaye."
Mustapha ya fara samun lambobin yabo a kan aikin da ya yi tare da makarantarsa.

Ya lashe kyautar gwarzon mai bayar da agaji ta "Robert Burns humanitarian award" ta 2016, wadda ake bai wa wadanda suka taimaka wajen kare rayuka ko suka kubutar da rayukan jama'a ko al'umma baki daya, ta hanyar sadaukar da kai."

An kuma ba shi lambar yabo ta "Aurora Prize Modern Day Hero award," ta 2017 na wadanda rayuwarsu da ayyukansu ke kare rayuwar wasu"
Haka kuma ya bayyana, mika 'yan matan Chibok 82 zuwa ga gwamnati, a matsayin "wata babbar nasara a rayuwata."

"Ina jin cewa na yi wani abu da duniya za ta yi alfahari da cewa lallai na yi abin a yaba," in ji Mustapha.
bbchausa.





No comments:

Post a Comment