Pages

Monday 10 July 2017

'Yanmata kurage yawan bata lokacinku a shafukan sada zumunta>>Sarkin Musulmi

Me alfarma sarkin musulmi,  Alhaji Sa'ad Abubakar yayi kira ga matasa, musamman 'yan mata dasu rage yawan bata lokacin da sukeyi akan kafofin sada zumunta da muhawara domin su mayar da hankali wajan karatu da sauran abubuwan da zasu amfani rayuwarsu.

Sarkin yayi wannan kirane a wajen kammala gasar karatun kur'ani ta kasa da aka kammala yace" abin takaicine irin yanda shafukan sada zumunta irinsu facebook instagram, 2go, whatsapp da sauransu ke daukewa matasa hankula musamman 'yan mata basa mayar da hankali wajen karatu da abubuwan da zasu amfanesu a rayuwa.

Yayi kira ga matan dasu rage yawan lokacin da suke batawa a irin wadannan shafuka domin yace mata sune kusan tushen tarbiyya da zamantakewa ta rayuwar al'umma da kuma kula da gida idan akace sun kauce to lallai al'umma zatashiga cikin matsala.

Sarkin yayi kira ga iyaye dasu saka ido kan 'ya 'yansu domin su rika kula da irin rayuwar da sukeyi a karfafamusu gwiwa su rika yin abubuwan da zasu amfanesu kamar su karatun alkur'ani dadai sauransu.

No comments:

Post a Comment