Pages

Monday 4 June 2018

Da alama Mohamed Salah zai buga gasar cin kofin Duniya: Ya fara nuna alamun warkewa

Ga dukkan alamu tauraron kwallon kafar Kasar Egypt/Misra, Mohmed Salah ya fara warwareya daga raunin kafadar saya samu kuma zai iya buga gasar cin kodin Duniya da za'a buga a kasar Rasha.


Tun bayan ciwon da yaji a wasan karshe na gasar cin kofin zakarun turai da sukayi taho mu gama shi da Ramos ake sa ran da wuya dan wasan zai iya warkewa har ya samu buga gasar cin kofin Duniya.

To amma sai gashi ya saka wannan hoton nashi a dandalinshi na sada zumunta na Twitter inda aka ganshi yana motsa jiki ta bangaren kafadar daya ji ciwon kuma ya rubuta ina jin dadi, alamar dake nuna cewa ya fara samun sauki.

Ba karamin murna tawagar kwallon kafar kasarshi zasu yi ba idan ya samu warkewa kamin fara gasar cin kofin Duniyar.

No comments:

Post a Comment