Pages

Monday 4 June 2018

Hukumar Tsaro Ta Farin Kaya (DSS) Ta Janye Jami'anta Masu Tsaron Lafiyar Saraki Da Dagora

Wannan ya zo kafin tattaunawar da za a yi tsakanin Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo da tawagar 'yan sabuwar PDP wadanda Dogara zai jagiranta ranar Litinin. 


Saraki ma mamba ne na tawagar sabuwar PDP, bangaren da suka balle daga jam'iyyar PDP a shekarar 2013 sannan suka hade da jam'iyya mai mulki ta APC kafin babban zaben 2015.

Jaridar "TheCable" ta fuskanci cewar an umarci jami'an tsaron da ke tsaron lafiyar manyan shuwagabannin majalisun guda biyu da nan take su bayyana a shelkwatar hukumar ta DSS.

Ba wani dalili da aka bada na janye jami'an, duk da cewa an yi imanin akwai hannun fadar shugaban kasa a ciki. 

Jaridar TheCable, bata iya samun tabbacin labarin daga Hukumar DSS, wacce bata da kakaki tun da aka nada Lawal Daura babban daraktanta a 2015 ba.

Koda yake dai majiyarmu daga Majalisar Tarayya ta tabbatar mana da labarin janye jami'an.

Ba da jimawa ba tawagar sabuwar PDP din ta zauna mitin da shugabannin APC inda take kokawa kan jam'iyya mai mulki na kaskantar da su bayan sun taimaka mata gurin kawar da PDP a zaben 2015.

Akwai hasashen cewar mambobin sabuwar PDP din za su balle daga jam'iyyar APC sannan su tsaida dan takara da zai kalubalanci Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a 2019.
Sarauniya

No comments:

Post a Comment