Pages

Monday 4 June 2018

Abin tausai: Karanta Yanda sojin Isra'ila suka mata kisan rashin Imani

Wannna wata bauwar Allah ce,  me bayar da agajin gaggawa ga wadanda suka ji rauni a gurin da ake arangama tsakanin falasdinawa da Yahudawan Isra'ila, sunan ta Razan Al-Najjar, kuma labarinta ya watsune dalilin kisan rashin Imanin da sojin Isra'ila suka mata.


Taje kaiwa wani da sojojin suka harba daukine, sai wani sojan Isra'ila, gwanin harbi daga nesa ya harbeta a kirji, aka garzaya asibiti da ita amma sai ta rasu, jama'a da yawa sun halarci jana'izarta ta yanda har babu gurin tsayuwa har saman gidaje aka rika hawa ana tsayuwa dan yi mata sallah.



Muna fatan Allah ya jikanta.

No comments:

Post a Comment