Pages

Wednesday 22 May 2019

A karon farko 'yan majalisar wakilan Amurka Musulmai sun shirya bude-baki a majalisa

A karon farko 'yam Majalisun wakilan Amurka Musulmai da suka hada da mai wakiltar Minnesotta Ilhan Omar, mai wakiltar Indiana Andre Carson da mai wakiltar Michigan Rashida Tlaib sun shirya taron bude-baki a zauren majalisar.


Taron bude-bakin da aka shirya da hadin gwiwar kungiyar lauyoyi Musulmai ta Amurka ya kasance na farko da aka shirya a zauren majalisar dokokin kasar.

'Yan majalisar wakilai da dama da ma'aikatan majalisar ne suka halarci bude-bakin a wannan wata mai albarka.

A jawabin da wakiliyar Michigan Tlaib ta yi ta bayyana cewar wannan taron bude-baki na da muhimmanci a tarihi. 
TRThausa.



No comments:

Post a Comment