Pages

Sunday 19 May 2019

Hukumar Tara Haraji ta tara naira tiriliyan 1.5 cikin watanni ukun 2019

Hukumar Tara Kudaden Harajin Cikin Gida (FIRS), ta bada sanarwar cewa ta tara naira tiriliyan 1.5 a watanni ukun farkon shekarar 2019 da mu ke ciki.


Shugaban FIRS, Babatunde Fowler ne ya bayyana haka ga wakilin Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN, a birnin New York, Amurka.

Ya ce kudaden harajin sun hada da harajin kudaden shiga da ba na bangaren harkokin man fetur da gas aba, wadanda ya ce sun haura wanda aka samu a watanni ukun farko na shekarar 2018 da kaso 11 bisa 100.

Fowler ya je New York ne domin taron da Majalisar Dinkin Duniya ta dauki nauyi a kan hanyoyin da za a toshe kafafe da kofofin da ake hada-hada da haramtatttun kudaden sata, ko wadanda ake samu ta hanyar manyan laifuka irin cinikin haramtattun kwayoyi da makamai.

Ya ce an samu naira tiriliyan 1.17 a watanni uku na farkon 2018. Yanzu kuma an samu naira tiriliyan 1.5, wato an samu kari na naira bilyan 330 kenan.

Hukumar FIRS dai tun farkon shekarar nan ta ce ta na sa ran tara kudaden shiga har naira tiriliyan 8 a cikin shekarar 2019.

Kenan naira tiriliyn 1.5 da aka tara a cikin watanni hudu, su na daidai da kashi 18.17 daga cikin 100 na adadin da ake neman tarawa.

Daga nan ya ce FIRS ta fara tirsasa wa mutane masu asusun ajiya har 50,000 wadanda ke tasarifi da da sama da naira bilyan 100, da su rika biyar haraji.

Fowler ya ce FIRS ta kuma yin shirin da harajin Jiki-magayi, wato VAT, na shekarar 2019 zai haura naira tiriliyan 1 na 2018.
Premiumtimeshausa.


No comments:

Post a Comment