Pages

Sunday 19 May 2019

Real Madrid ta kammala kakar wasan 2018/19 da rashin nasara: Rashin saka Bale a wasan karshe ya jawowa Zidane Allah wadai

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta kare kakar wasan 2018/19 da rashin nasara a hannun Real Betis inda a wasan da suka buga na yau suka tashi Betis na cin 2-0. Saidai rashin saka Gareth Bale a wasan ya dauki hankula inda akai ta caccakar Zidane akai.



Ana dai rade-radin cewa Bale zai bar Madrid inda ake alakantashi da komawa Manchester United da wasa kuma ana kallon wasan na yau a matsayin wasanshi na karshe a kungiyar Madrid.

Saidai tun kamin take wasan, kocin kungiyar, Zinedine Zidane ya bayyana cewa koda zai yi canjin mutun 4 ba zai saka Bale ba a wasan, wannan magana da yayi tasa da dama suka ga cewa ba'a girmama Bale din ba dan kuwa ya kamata a bashi damar yin bankwana da magoya bayan kungiyar.

Koda bayan kammala wasan, Zidane ya kara fadar cewa shi keda ikon saka dan wasan da yake so ya saka kuma Bale yayi wa kungiyar kokari a baya amma na maganar yanzu ne

No comments:

Post a Comment