Pages

Sunday 19 May 2019

Messi ya ci kwallo ta 50 a kakar wasan bana: Karanta sauran tarihin da ya kafa

Tauraron dan kwallon kasar Argentina me bugawa Barcelona wasa, Lionel Messi ya zura kwallaye 51 a kakar wasa ta bana. Kwallayen nashi sun kai 51 a yau a wasan da Barcelona ta buga da Eibar inda yaci kwallaye 2 cikin minti 2.



A yanzu yawan kwallayen Messi a Laliga sun kai 36. Sannan yana da kwallaye 12 da ya ci a gasar Champions League da kuma kwallaye 2 da yaci a Copa Del Rey, da kuma kwallo daya a Joan Gamper Tropy.

A yanzu dai Messi zai lashe takalmin zinare na 6 kenan a tarihin buga kwallonshi.

Sannan ya shafe kakannin wasanni 6 kenan yana cin kwallaye fiye da 50, ya kafa irin wannan tarihi a kakannin wasa:

2010/11: 53
2011/12: 73
2012/13: 60
2014/15: 58
2016/17: 54
2018/19: 51

A kakar wasa ta bana dai Messi yana gaba da Benzema da Suarez da suke matsayi na biyu a yawan cin kwallaye a gasar laliga da yawan kwallaye 15 kenan. Wani zai iya cewa ai wadannan 'yan wasa sun yi fama da jiyya, to a gaskiya koda basu je jiyya ba ba karamar dagiya zasu ba kamin ace sun kamo Messin.

Messi yafi kungiyar Villadolid yawan kwallaye a kakar wasan bana inda ta ci kwallaye 32.

No comments:

Post a Comment