Pages

Tuesday 21 May 2019

Yayin da Nabaraska ya maka Hadiza Gabon a kotu: Karanta abinda tace akanshi


Labarai sun watsu sosai cewa, tauraron fina-finan Hausa, Mustafa Nabaraska ya maka abokiyar aikinshi, Hadiza Gabon a kotu inda har aka yi zaman kotun ba tare da Hadizar ta halarta ba, dalilin da yasa wani sabon labarin ya fito dake cewa kotu tasa a kamo mata Hadizar.


A yayin da ake tsaka da wannan labari, Hadizar ta saka hoton Mustafa Nabaraska a shafinta na Instagram inda ta rubuta, Babban yarinya sunan wani fim.

Wannan abu ya dauki hankula sosai, inda da dama suka mai kallon yanayin cewa watakila an yi sulhu ne tsakanin taurarin biyu.



No comments:

Post a Comment