Pages

Saturday 22 June 2019

A karshe dai kasar Amurka ta kaiwa kasar Iran Hari

 A yayin da hankulan Duniya suka karkata kan lamarin fadan dake shirin barkewa tsakanin kasashen Iran da Amurka bayan da kasar ta Iran ta kakkabo wani jirgin yakin Amurkar da tace yana mata leken Asiri, da farko dai Trump yayi barazanar kai hari amma ya fasa, saidai a karshe Amurkar ta kaiwa Iran din hari.



Rahoton Yahoo ya bayyana cewa, Hukumar kula da kwamfutoci da harin da ake kaiwa kasar ta kaiwa wata kungiyar 'yan kasar ta Iran dake leken asiri hari ta kwamfuta.

Kungiyar 'yan kasar ta Iran din wanda aka zargesu da taimakawa Iran wajan kaiwa tankokin man Ruwa hari ne kasar Amurka ta kaiwa harin, kamar yanda rahoton ya bayyana.

No comments:

Post a Comment