Pages

Tuesday 25 June 2019

An kai mummunan hari da jirgin yaki a filin tashi da saukar jiragen saman Saudiyya

Mutum daya ya ransa ransa inda wasu 7 suka jikkata sakamakon harin da aka kai a filin tashi da saukar jiragen sama na Abha dake Saudiyya.


Tashar Al-Arabiyya ta Saudiyya ta fadi cewa a harin da ake tunanin an kai da jirgin sama mara matuki an jikkata mutane 8 dake wajen ajje motoci na filin tashi da saukar jiragen sama na Abha.

Wani dan kasar Siriya dake zaune a Saudiyya da ya jikkata ya mutu a asibitin da aka kai shi.

Babu wata sanarwa da mahukuntan Saudiyya suka fitar game da harin.

A ranar 12 ga Yuni ma 'yan tawayen Houthi na Yaman sun kai hari a filin tashi da saukar jiragen sama na Abha tare da jikkata mutane 26.

A 'yan shekarun nan mayakan na Houthi na yawan kai wa Saudiyya hare-hare da makamai masu linzami.
TRThausa.


No comments:

Post a Comment