Pages

Tuesday 25 June 2019

Man United ta yi watsi da tayin PSG kan musayar Neymar da Pogba

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta ki amincewa da tayin kungiyr kwallon kafa ta PSG wadda ta nemi su yi musayar Neymar da Pogba.



Dukkanin ‘yan wasan biyu dai wato Neymar Junior da Paul Pogba na son rabuwa da kungiyoyin da su ke taka leda cikin wannan kakar musayar ‘yan wasan, sai dai bayanai na nuni da Pogba na son komawa Real Madrid ne yayinda shi kuma Neymar ke fatan komawa kungiyarsa ta baya wato Barcelona.

Rahotanni sun bayyana cewa United ta ki amincewa da batun musayar Neymar ne bisa dalili biyu kamar yadda mataimakin shugaban Club din Ed Woodward ya sanar, na farko kuwa shi ne United na fatan ci gaba da zama da Pogba, na biyu kuma albashin Neymar na yuro dubu dari 9 a kowanne mako zai shafi tattalin arzikin Club din.


Shekara guda kenan Pogba na yunkurin rabuwa da United amma hakansa ba ta cimma ruwa, tun bayan sauya shekarsa daga Juventus kan yuro miliyan 89 a shekarar 2016.
RFIhausa.

No comments:

Post a Comment