Pages

Wednesday 26 June 2019

Atiku ya taya Super Eagles murnar kaiwa mataki na gaba a gasar Nations Cup


Dan takarar shugaban kasa a zaben 2019 Atiku Abubakar ya bayyana farin cikinshi da kasancewar Najeriya tsallakewa zuwa matakin wasa na gaba a gasar cin kofin nahiyar Afrika dake gudana a kasar Egypt.

Da yake bayyana farin cikinshi a shafinshi na Twitter, Atiku Abubakar ya bayyana cewa, yayi farin ciki da zuwan Najeriyar matakin kasashe 16 da zasu buga wasan neman zuwa matakin kusa dana karshe duk cewa akwai wasa daya daya rage musu, yace tafiya sannu-sannu kwana nesa.

No comments:

Post a Comment