Pages

Tuesday 25 June 2019

Bamu samun wasu kudin garabasa: Kakakin majalisar dattawa ya bayyana nawane Albashinshi

Kakakin majalisar dattijai,Ahmad Lawal ya bayyana yawan Albashin da yake dauka inda yace daga shi babu wasu kudin garabasa da 'yan majalisar ke karba kamar yanda wasu 'ya  Najeriya ke tunani.



Lawal ya Bayyana hakane a ganawar da yayi da kungiyar 'yan majalisar da suka kaimai ziyarar ban girma a ofishinshi.

Yace Albashina dubu 750 nake dauka hakanan kuma sauran 'ya  majalisa na daukar nasu albashin amma babu wasu kudin garabasa da wasu 'yan Najeriya ke tunain muna samu.

Ya kara da cewa amma a matsayina na sanata ina bukatar a gyaramin ofishina da sauran kayan aikin da nake bukata dan aikina ya tafi daidai.




Lawal ya sha alwashin ci gaba da bayyanawa 'yan Najeriya yanda majalisar take aiki inda yace sun cancanci sanin yanda ake gudanar da dukiyarsu.

Ya kuma bukaci samarwa da majalisar isassun kudi dan gudanar da ayyukanta yanda ya kamata.

No comments:

Post a Comment