Pages

Saturday 15 June 2019

'Yan majalisar tarayya zasu kashewa kansu Naira Biliyan 19.89 cikin watanni 3


Rahotanni sun bayyana cewa, 'yan majalisar tarayya da aka rantsar kwanannan zasu kashe Naira biliyan 19. 89 wajan hidindimunsu.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa, 'yan majalisar zasu kashe Naira Biliyan 4.68 a matsayin kudin maraba da zasu yi amfani dasu wajan kama gurin zama da kuma kayan daki-Ofis.

Sannan kowane daga majalisar dattijai 109 zai samu miliyan 40.5 cikin watanni 3 dan yin amfani dasu wajan al'amuran yau da kullun hakanan suma 'yan majalisar wakilai kowane daga cikin 360 zai samu miliyan 30.


No comments:

Post a Comment